logo

HAUSA

Shugaba Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Shugaban Kasar Gambia

2021-12-24 20:23:52 CRI

Shugaba Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Shugaban Kasar Gambia_fororder_gambia

A yau Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga shugaban Gambia Adama Barrow, bisa sake zaben sa da aka yi a matsayin shugaban kasa.

Cikin sakon na sa, shugaba Xi ya ce tun bayan dawo da huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Gambia, sassan biyu ke zurfafa amincewa ta fuskar siyasa, sun kuma cimma manyan nasarori a fannonin hadin gwiwar su, kaza lika sun fahimci juna, tare da taimakawa juna a dukkanin al’amuran dake shafar manyan muradun su.

Shugaba Xi ya kara da cewa, yana dora matukar muhimmanci kan ci gaban dangantakar sassan biyu, kuma a shirye yake ya ci gaba da aiki da bangaren Gambia, wajen zurfafa hadin gwiwa da mahukuntan kasar, da ma hadin gwiwar kasar sa da sassan Afirka, karkashin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, ta yadda Sin da Gambia da al’ummun su, za su ci gaba da cin gajiyar dangantakar su.   (Saminu)

Saminu