logo

HAUSA

Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin karfafa dokokin jam’iyya domin kare jagoranci da gudanar da gwamnati cikin nasara

2021-12-20 19:50:08 CRI

Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin karfafa dokokin cikin gida na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ta yadda hakan zai ba da damar kare jagorancin ta, da kuma gudanar da gwamnati cikin nasara. Xi Jinping, ya ce wajibi ne a tabbatar da kare tsarin gudanarwa na tsakiya, da dunkule sassan jagorancin kwamitin kolin JKS.

Ya ce wadannan dokoki, su ne za su ingiza dorewar salon shugabancin jam’iyyar a tsawon lokaci, da kuma ikon kasar na jure matakan aiwatar da manufofin ci gaba da daidaito.

Shugaban na Sin, wanda kuma shi ne shugaban hukumar zartaswa na rundunar sojojin kasar, ya yi wannan tsokaci ne cikin wani umarni da ya bayar, lokacin da ya halarci taron kasa game da tattauna dokokin cikin gida na JKS, wanda ya gudana a Litinin din nan a birnin Beijing.  (Saminu)

Saminu