logo

HAUSA

Shugaba Xi ya aike da sakon ta’aziyyar wadanda mahaukaciyar guguwar Rai ta halaka a Philippines

2021-12-21 20:47:19 CRI

Shugaba Xi ya aike da sakon ta’aziyyar wadanda mahaukaciyar guguwar Rai ta halaka a Philippines_fororder_634b0a05-f0f7-4b3e-a0dd-c8fcbea2238c

A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyyar wadanda mahaukaciyar guguwar Rai ta halaka, ga takwaransa na kasar Philippines Rodrigo Duterte.

Shugaba Xi, ya ce ya kadu da jin labarin irin hasarar rayuka da dukiyoyi da guguwar mai hade da mamakon ruwan sama ta haddasa a makon jiya. Ya ce a madadin gwamnatin kasar Sin, da al’ummar kasar, da shi kan sa, yana mika sakon ta’aziyya ga ‘yan uwan wadanda wannan ibtila’i ya shafa, tare da jajantawa, da kuma fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

Shugaban na Sin, ya ce a shirye kasar Sin take ta taimakawa Philippines gwargwadon ikon ta. Ya ce yana da imanin yankin da wannan bala’i ya aukawa zai kai ga shawo kan lamarin, tare da sake ginuwa. (Saminu)

Saminu