logo

HAUSA

Shugaban Kasar Sin Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 40 Da Kafuwar Yankin Tattalin Arziki Na Musamman Na Xiamen

2021-12-21 20:32:35 CRI

Shugaban Kasar Sin Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 40 Da Kafuwar Yankin Tattalin Arziki Na Musamman Na Xiamen_fororder_src=http___nimg.ws.126.net__url=http%3A%2F%2Fdingyue.ws.126.net%2F2021%2F0621%2F70221c12j00qv0ra4003lc000u000exc&thumbnail=650x2147483647&quality=80&type=jpg&refer=http___nimg.ws.126

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murnar cika shekaru 40 da kafuwar yankin tattalin arziki na musamman na Xiamen na lardin Fujian dake gabashin kasar Sin.

Cikin wasikar ta sa da aka karanta, shugaba Xi, ya jinjinawa tarihi da yankin tattalin arziki na musamman na Xiamen ya kafa cikin wadannan shekaru 40, yana mai cewa yankin ya samar da muhimmiyar gudummawa ga manufar kasar Sin ta aiwatar da sauye-sauye a gida, da bude kofa ga waje, da zamanantar da salon gurguzu, ya kuma taka rawar gani wajen yayata manufar dinke kasar Sin.

Daga nan sai ya yi kira ga mahukuntan tattalin arziki na musamman na Xiamen da su tsaya tsayin daka kan hanyar gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin, tare da jajircewa wajen samar da sabbin ci gaba, da bin sabbin dabarun bunkasuwa, tare da aiki tukuru da hade yankin da sauran sabbin dabarun ci gaba.

Ya ce ya zama wajibi a kara kaimi wajen zurfafa sauye-sauye, da bude kofa a dukkanin sassan, da ingiza ci gaba mai gamsarwa, da kara hade sassan ci gaba masu alaka da zirin Taiwan biyu, kana a yi aiki haikan wajen shigewa gaba don cimma nasarar zamanantar da gurguzu yadda ya kamata.  (Saminu)

Saminu