logo

HAUSA

Shugaba Xi Ya Gana Da Wakilan Al’umma Masu Ba Da Gudummawa Ga Wanzar Da Zaman Lafiya A Sin

2021-12-16 13:47:45 CRI

Shugaba Xi Ya Gana Da Wakilan Al’umma Masu Ba Da Gudummawa Ga Wanzar Da Zaman Lafiya A Sin_fororder_xi

A jiya Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da wakilan al’umma, da suke ba da gudummawa ga wanzar da zaman lafiya a kasar Sin, inda ya yaba musu bisa irin kokarin da suke yi a wannan fanni.

Yayin zaman wanda ya gudana a nan birnin Beijing, shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren koli na kwamitin tsakiyar JKS, kuma shugaban hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar, ya jinjinawa nasarori da wakilan suka cimma, tare da karfafa musu gwiwar ci gaba da kara azama, wajen gina gagarumin tsarin wanzar da zaman lafiya a kasar.   (Saminu)

Saminu