logo

HAUSA

Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Jama'ar Kasar Sin Murnar Cika Shekaru 80 Da Fara Watsa Shirye-shirye Ga Kasashen Waje

2021-12-03 19:29:09 CRI

Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Jama'ar Kasar Sin Murnar Cika Shekaru 80 Da Fara Watsa Shirye-shirye Ga Kasashen Waje_fororder_cmg

Yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasika don taya jama’ar kasar Sin murnar cika shekaru 80 da fara watsa shirye-shirye ga kasashen ketare. Xi ya kuma mika godiya ga ma’aikatan babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da abokai na kasashen waje, wadanda suka tallafawa kafar watsa shirye-shiryen jama'ar kasar Sin ta ketare.

Xi Jinping ya nuna a cikin wasikar cewa, tsawon shekaru 80, a karkashin jagorancin JKS, kafar watsa shirye-shirye ta kasashen waje ta ci gaba da gudanar da al'adun gargajiya, ba ta manta da ainihin manufarta, da yada shawarwarin jam'iyyar ba, da sa kaimi ga yada ci gaban kasar Sin gaba daya, ta kuma yada labarai gami da muryar kasar Sin ga duniya.

Xi Jinping ya jaddada fatan cewa, za ku ci gaba da fito da sabbin fannoni da yin kirkire-kirkire, da inganta hanyoyin sadarwa na kasa da kasa, da samar da sabbin kafofin watsa labaru da babu kamar su a duniya masu karfin jagoranci, da sadarwa, da yin tasiri, da samar da sabbin ra'ayoyi don tabbatar da mafarkin kasar Sin, da sake farfado da al'ummar kasar Sin, da sa kaimi ga gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama.  

A ranar 3 ga watan Disamba na shekarar 1941 ne, JKS ta kafa tashar watsa labarai ta Yan'an a harshen Japananci, wanda ke nuna yadda jama'ar kasar Sin suka kafa hidimar watsa shirye-shirye ga kasashen waje. A halin yanzu, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin, yana watsa shirye-shiryensa ga ketare cikin harsuna 44 .(Ibrahim)

Ibrahim