logo

HAUSA

Xi: Fahimtar Kasar Sin Na Bukatar Fahimtar JKS

2021-12-02 19:47:24 CRI

Xi: Fahimtar Kasar Sin Na Bukatar Fahimtar JKS_fororder_xjp

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana Alhamis din cewa, idan har ana son fahimtar kasar Sin a yau, wajibi ne a yi kokarin fahimtar JKS.

Xi ya bayyana haka ne, lokacin da yake gabatar da jawabi ta kafar bidiyo a yayin bude taron fahimtar kasar Sin na shekarar 2021 dake gudana a birnin Guangzhou na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, duniya na fuskantar sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin karni, wadanda suka hada da cutar COVID-19, da suka sanya duniya cikin yanayi na kunci.

Ya kara da cewa, yana da muhimmanci mu kara yin musayar ra'ayi, da mu'amala da hadin gwiwa, da ba da gudummawar hikima da karfinmu, wajen tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta a irin wannan yanayi.

Xi ya ce, kamar yadda na nuna, idan har ana son fahimtar kasar Sin a yau, dole ne a yi kokarin fahimtar JKS. Ya sanar da cewa, a bana ne JKS ta cika shekaru 100 da kafuwa. Yana mai cewa, JKS ta yi nasarar hada kai tare da jagorantar jama'ar kasar Sin, har aka kai ga kawo sauyi ga makomar jama'ar kasar Sin baki daya, da ma yadda hakan ya yi tasiri sosai kan tarihin duniya a cikin karni shekaru 100 da suka gabata. (Ibrahim)

Ibrahim