logo

HAUSA

Mutane 4 sun mutu, wasu 12 sun ji rauni a hadarin jirgin kasa a Ghana

2021-12-19 17:06:40 CRI

A kalla mutane hudu ne suka mutu kana wasu 12 sun samu raunuka bayan da jiragen kasa biyu suka yi taho mu gama a shiyyar Western Region na kasar Ghana, kamar yadda hukumar ‘yan sandan kasar ta tabbatar.

Sebastian Folivie, jami’in hukumar ‘yan sandan shiyyar Western Region, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, hadarin ya faru ne a tsakanin wasu manyan jiragen kasa biyu inda suka yi karo da juna a hanyar jirgin kasa ta Tarkwa zuwa Kojokrom a tsakar daren ranar Juma’a.

Ya ce, guda daga cikin jiragen kasan ya gamu da matsalar birki ne inda ya haura kan daya jirgin a kusa da unguwar Wassa Manso.

Jami’in dan sandan ya ce, an tura masu aikin ceto daga hukumar kashe gobara ta kasar Ghana cikin hanzari zuwa inda lamarin ya faru, kuma ma’aikatan sun yi nasarar raba jiragen dake manne da juna.

Ya ci gaba da cewa, uku daga cikin mutanen da suka samu raunuka an riga an sallame su daga asibitin bayan duba lafiyarsu, yayin aka kai gawar mutanen hudu da suka mutu zuwa dakin aje gawarwaki dake asibitin da ake jinyar wadanda suka samu raunukan.

A cewar jami’in, ‘yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike don tabbatar da hakikanin musabbanin hadarin.(Ahmad)

Ahmad