logo

HAUSA

Hukumar kwallon kafan Ghana ta fara bincike game da zargin magudin wasa

2021-07-22 11:15:29 CMG

Hukumar kwallon kafan Ghana ta fara bincike game da zargin magudin wasa_fororder_ibrahim-3

Hukumar kwallon kafan Ghana(GFA) ta sanar a jiya Laraba cewa, ta fara gudanar da bincike game da shirya magudin wasa, da ake zargin wasu kungiyoyin wasan firimiyar kasar biyu da kitsawa, a zagayen karshe na wasannin lig din kasar na shekarar 2020/2021.

Hukumar ta ce, tana sanar da jama’a da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa cewa, hukumar ba za ta bayar da duk wata takardar shaidar sauya kulob na kasa da kasa, da takardar gabatarwa ga duk wani ofishin jakadanci don neman biza ga duk wanda wannan bincike ya shafa ba, har sai ta kammala gudanar da binciken.

Kulob din kwallon kafa na AshantiGold SC ne, ya doke kulob din Inter Allies, wanda tuni ya fadi a kasan teburin gasar, da ci 7 da nema, a wasan karshe na gasar Lig din kasar, da aka buga a karshen mako.(Ibrahim)

Ibrahim