logo

HAUSA

Ghana zata fara hada-hadar kudi ta intanet a watan Satumba

2021-07-10 16:37:39 CMG

Ghana zata fara hada-hadar kudi ta intanet a watan Satumba_fororder_ghana

Kasar Ghana za ta kaddamar da hada-hadar kudi ta intanet karon farko, a watan Satumba.

Mataimaki na 1 na Gwamnan babban bankin kasar wato Maxwell Opoku-Afari ne ya bayyana haka, cikin jawabin da ya gabatar yayin wani taron yini biyu, na wayar da kan ‘yan jarida na bangaren hada-hadar kasuwanci.

A cewarsa, bullo da hada-hadar kudi ta intanet, daya ne daga cikin dabarun da suka wajaba bayan annobar COVID-19, domin annobar ta gaggauta ingiza fara hada-hada ba tare da amfani da tsabar kudi ba, kuma ana sa ran shirin zai kawo ci gaba ga tsarin hada-hadar kudi a kasar.

Ya ce shirin wani bangare ne dake tabbatar da bankin ya aminta da bukatar dake akwai ta gudanar da harkokin da suka shafi biyan kudi da sauran hidimomin kudi ta intanet. Yana mai cewa, wannan zai ba bankin damar samar da dandalin da zai karawa hada-hadar kudi ta intanet daraja.

Ya Kara da cewa, tsawon lokacin da kashin farko na shirin zai dauka, ya dogara ne da yadda mutane suka karbe shi da kuma yadda harkokinsa za su gudana da ma yadda za a tunkare kalubalen da ka iya tasowa. (Fa’iza Mustapha)

Fa'iza