logo

HAUSA

Ghana ta jingine shirin gina sabon filin wasan gasar kasashen Afrika

2021-07-02 11:35:17 CMG

Ghana ta jingine shirin gina sabon filin wasan gasar kasashen Afrika_fororder_ahmad-4

Kasar Ghana ta dakatar da shirinta na gina sabon katafaren filin wasannin motsa jiki domin karbar bakuncin gasar wasannin kasashen Afrika ta All-African Games a shekarar 2023, kamar yadda majalisar dokokin kasar ta sanar a jiya Alhamis.

Sanarwar tace, ministan matasa da wasanni na kasar, Mustapha Ussif, ya fadawa majalisar dokokin kasar cewa, maimakon hakan, kamata ya yi a kammala aikin ginin wani sabon filin wasan dake Borteyman kusa da tashar ruwan gabashin birnin Tema, kana kamata ya yi kasar ta yi kwaskwarima ga filin wasan wanda aka yi watsi da shi dake jami’ar kasar Ghanan gabanin shirya gasar.

Ministan ya danganta sauyin da aka samu da karancin lokaci wanda ya faru sakamakon annobar COVID-19.

Sannan kuma, ministan ya baiwa majalisar dokokin kasar tabbacin aniyar gwamnati na kokarin tanadin dukkan muhimman kayayyakin da ake bukata domin karbar bakuncin gasar.

Haka zalika, ya kara da cewa, kasar Ghana a shirye take ta karbi bakuncin gasar wasannin a shekarar 2023, kuma za ta yi amfani da sabbin kayayyakin tare da yin kwaskwarima ga sauran kayayyakin da ake bukata.

Ghana za ta karbi bakuncin gasar wasannin wacce kasashe 54 zasu halarta a gasar ta All-African Games karo na 13 a shekarar 2023.(Ahmad)

Ahmad