logo

HAUSA

Ghana za ta bayyana bukatun Afrika a taron kwamitin sulhun MDD

2021-06-27 17:22:28 CRI

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya ce, kasar sa za ta yi amfani da damar ta ta wakilcin kwamitin sulhun MDD UNSC domin bayyana bukatun tsaro dake damun Afrika, fadar shugaban kasar Ghana ta bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Shugaban ya ce, kasar ta yammacin Afrika za ta yi amfani da matsayin ta na zabar ta da aka yi a matsayin mai wakilcin wucin gadi a kwamitin sulhun MDD domin nemawa kasashen Afrika hanyar da za a samu dawwamman tsarin warware matsalolin tsaro dake addabar nahiyar.

A cewar shugaban, kasar Ghana za ta ci gaba da karfafa tuntuba da nufin tattauna bukatun Afrika a gaban kwamitin na UNSC da nufin tabbatar da nahiyar tana magana da murya mai karfi a wannan mataki.

Akufo-Addo ya bayyana cewa, matsalolin ta’addanci a yankin Sahel da ayyukan ‘yan fashin gabar tekun Guinea na cikin batutuwan tsaro dake damun nahiyar, wadanda kasar Ghana take burin gabatarwa a gaban kwamitin sulhun MDDr.

Shugaban ya kara da cewa, matsalar ‘yan fashin teku tana matukar haifar da mummunar hasara a fannin shigo da kayayyaki daga kasashen ketare zuwa kasashen yammacin Afrika sakamakon tsadar kudaden inshora wanda ake biya ga ayyukan sufurin kayayyaki ta ruwa. Jiragen ruwan dakon kaya suna matukar fuskantar barazanar hare haren ‘yan fashin tekun.

Ya bukaci a warware batutuwan dake shafar Afrika a cikin nahiyar ta hanyar lumana, musamman batun takaddamar dake tsakanin kasashen Habasha, Sudan da Masar kan tekun Nile.(Ahmad)

Ahmad