logo

HAUSA

An yi bitar dabarun kasar Sin na yaki da talauci yayin taron karawa juna sani na hadin gwiwar kasashe masu tasowa

2021-10-22 10:30:42 cri

An yi bitar dabarun kasar Sin na yaki da talauci yayin taron karawa juna sani na hadin gwiwar kasashe masu tasowa_fororder_src=http___n.sinaimg.cn_news_transform_220_w1100h720_20181114_cd71-hnvukfe9937195&refer=http___n.sinaimg

Kwararru daga kasar Sin da na kasashen ketare da shaihunnan malamai, sun zurfafa tattaunawa game da dabarun da kasar Sin ta yi amfani da su, wajen cimma nasarar yaki da talauci da hadin gwirwar kasa da kasa a fannin.

Kungiyar masana harkokin zamantakewa ta kasar Sin CASS, da ofishin MDD mai kula da ci gaban kasashe masu tasowa ko UNOSSC ne suka yi hadin gwiwar shirya taron, wanda ya gudana a jiya Alhamis ta kafar bidiyo da kuma zahiri.

Da yake tsokaci yayin taron, shugaban CASS Xie Fuzhan, ya ce Sin na da kwarewa wajen aiwatar da matakan kawar da kangin talauci, wanda hakan jigo ne na wanzar da ci gaba, da ingiza manufar nan ta gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil adama.

Wakilai daga hukumomin kasa da kasa, ciki har da na shirin samar da ci gaba na MDD, da gungun kwararru na kasashe masu tasowa, sun yi musayar yawu game da hanyoyin rage fatara, da hanyoyin da kasashe daban daban suka bi wajen cimma nasarar hakan, da ma sauran wasu batutuwa.

Kaza lika yayin taron, CASS da UNOSSC sun sanya hannu kan takardar fahimtar juna, ta kafa shirin hadin gwiwa a hukumance.  (Saminu)