logo

HAUSA

MDD ta yi tir da harin da aka kai wa jami’an wanzar da zaman lafiya

2021-10-03 16:07:20 CMG

MDD ta yi tir da harin da aka kai wa jami’an wanzar da zaman lafiya_fororder_1

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kakkausar suka kan harin da aka kai wa jerin gwanon motocin jami’an wanzar da zaman lafiya na majalisar dake Mali. An kai harin na ababen fashewa ne jiya Asabar, a kusa da kauyen Tessalit na yankin Kidal, inda ya yi sanadin mutuwar jami’i daya dan kasar Masar, yayin da wasu 4 suka ji munanan raunuka.

Sakatare Janar din ya jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su, tare da gwamnati da al’ummar Masar. Haka kuma ya yi wa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya cikin gaggawa.

Sanarwar da kakainsa Stephane Dujarric ya fitar dangane da lamarin, ta ruwaito Antonio Guterres na cewa, hari kan jami’an wanzar da zaman lafiya ka iya zama laifin yaki karkashin dokokin kasa da kasa, yana mai kira ga hukumomin kasar Mali da kada su yi kasa a gwiwa wajen gano wadanda ke da hannu wajen kai hare-haren tare da tabbatar da hukunta su. (Fa’iza Mustapha)

Faeza