logo

HAUSA

Wang Yi: An Cimma Matsaya Kan Dangantaka Da Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Taron FOCAC

2021-12-01 20:07:38 CRI

Wang Yi: An Cimma Matsaya Kan Dangantaka Da Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Taron FOCAC_fororder_focac

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana a jiya Talata cewa, Sin da kasashen Afirka sun cimma matsaya mai muhimmanci, kan dangantakar dake tsakaninsu a gun taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC).

Wang ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwararsa ta kasar Senegal Aissata Tall Sall bayan kammala taron. Yana mai cewa, za a iya takaita muhimman batutuwa guda biyar masu muhimmanci da Sin da Afirka suka cimma kamar haka.

Na farko, bangarorin biyu za su bunkasa ruhin abokanta da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Shugaba Xi Jinping ne ya fara gabatar da shawara a cikin jawabinsa, kuma ya zama wani muhimmin batu a taron.

Na biyu, Sin da Afirka za su yi aiki tare, don shawo kan annobar COVID-19. A jawabin da ya gabatar a yayin bude taron, shugaba Xi ya sanar da cewa, kasar Sin za ta samar da karin alluran rigakafin COVID-19 biliyan 1 ga kasashen Afirka. Wannan shi ne shiri mafi girma na taimakon rigakafi da wata kasa guda ta samar wa Afirka tun bayan barkewar annobar, wanda ko shakka babu, zai karfafawa kasashen Afirka gwiwa wajen shawo kan annobar.

Na uku, bangarorin biyu za su yi kokarin inganta hadin gwiwar Sin da Afirka. Haka kuma, shugaba Xi ya sanar da cewa, kasar Sin, za ta aiwatar da wasu shirye-shirye guda 9 tare da hadin gwiwar kasashen Afirka, wannan wani babban batu ne dake kara bayyana kudirin kasar Sin kan Afirka da ma kara bunkasa alakar sassan biyu.

Na hudu, bangarorin biyu za su yi aiki tare don aiwatar da tsarin kasancewar bangarori daban-daban bisa gaskiya.

Na biyar, Sin da kasashen Afirka za su yi hadin gwiwa, wajen gina al'ummar Sin da Afirka mai makoma ta bai daya a sabon zamani.(Ibrahim)

Ibrahim