logo

HAUSA

Sin ta ba da gudummawar sama da ton 400 na shinkafa ga Sudan ta Kudu

2021-12-16 10:34:37 CRI

Sin ta ba da gudummawar sama da ton 400 na shinkafa ga Sudan ta Kudu_fororder_shinkafa

Ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Sudan ta Kudu a ranar Laraba 15 ga wata ya bayar da tallafin don 416 na shinkafa a matsayin agajin gaggawa na abinci ga jahohin da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a kasar.

Manase Lomole, shugaban hukumar samar da agaji na kasar, ya bayyana cewa, gudummawar kasar Sin ta nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da taimakawa al’ummar kasarsa mafi yarinta a duniya.

Ya kara da cewa, tun a shekarar da ta gabata, Sudan ta Kudu ta gamu da mummunar ambaliyar ruwa wadda ba a taba ganin irinta ba a shekaru sama da sittin, inda mutane sama da 800,000 ambaliyar ruwan ta shafa a jahohi 10, yayin da wasu mutane kusan miliyan 11 har yanzu suke fama da matsalar karancin abinci.

Lomole ya gode wa kasar Sin bisa samar da tallafin da kuma gudummawar da take baiwa kasar na kayayyakin kiwon lafiya da ayyukan hidimar tallafin jin kai a kasar. A cewar Lomole, kasar Sin ba ta takaita wajen tallafawa Sudan ta Kudu ta bangaren hidimar tallafin jin kai ba, har ma a fannin kiwon lafiya.(Ahmad)

Ahmad