logo

HAUSA

MDD ta saki kudaden gaggawa domin mayar da martani ga ambaliyar ruwa a Sudan ta Kudu

2021-11-23 10:37:42 CRI

MDD ta saki kudaden gaggawa domin mayar da martani ga ambaliyar ruwa a Sudan ta Kudu_fororder_211123-yaya-5-Ambaliyar ruwa a Sudan ta kudu

Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD ko OCHA a takaice, ya bayyana a jiya Litinin cewa, mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin jin kai da bayar da agajin gaggawa Martin Griffiths, ya ware dalar Amurka miliyan 13 daga asusun ba da agajin gaggawa na majalisar, domin daukar matakan gaggawa kan bala'in ambaliyar ruwa da ta abkawa Sudan ta Kudu

OCHA ya ce kimanin mutane 809,000 ne ambaliyar ruwa ta shafa a sassa da dama na kasar, baya ga karuwar tashe-tashen hankula dake addabar wasu yankunan kasar kamar Tambura.

Hukumomin agajin jin kai dai sun kara kaimi, don biyan bukatun mutanen da matsalar ta shafa. Shekara ta uku ke nan a jere da ambaliyar ruwa take mamaye yankuna da dama na Sudan ta Kudu.

A cewar OCHA, kudaden sun taimaka wajen daukar matakai kan daya daga cikin ambaliya mafi muni kuma wadda ta dauki lokaci mai tsawo. Hukumomin MDD da abokan huldarsu, za su ba da agajin jin kai da kariya ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa, wadanda ke da karanci ko ma ba su da muhimman kayayyakin amfanin yau da kullun. (Ibrahim)