logo

HAUSA

Tawagar likitocin kasar Sin sun sassauta nauyin da gidan marayu na Sudan ta Kudu ke fama da shi

2021-11-22 09:26:46 CRI

Tawagar likitocin kasar Sin sun sassauta nauyin da gidan marayu na Sudan ta Kudu ke fama da shi_fororder_1122-S.Sudan-Ibrahim

A baya, masu kula da gidan marayu na Confident Children Out of Conflict (CCC) da ke Juba, babban birnin Sudan ta Kudu, su kan kashe dalar Amurka 1,500 a duk wata wajen kula da lafiyar marayu 61 da ke zaune a wurin, amma sakamakon kasancewar tawagar likitocin kasar Sin, lamarin ya canja matuka.

Babbar darektar CCC Hellen Murshal Boro, ta yaba wa tawaga ta tara ta rukunin likitocin kasar Sin da suka ziyarci gidan marayun a ranar Lahadin da ta gabata, kan yadda suka taimaka wajen rage kudaden da ake kashewa wajen kula da yara masu fama da cutar zazzabin cizon sauro da sauran cututtuka.

Boro ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Juba, bayan da ta karbi wasu magunguna da abinci daga tawagar likitocin da suka kawo ziyara cewa, muna da yara a nan da suke fama da rashin lafiya kamar cutar HIV/AIDS. Don haka, yayin da magungunan cutar kanjamau suka kasance kyauta, maganin zazzabin cizon sauro kuma ba kyauta ba ne saboda tsadarsu

Ta kara da cewa, ko da yake asusun tallawafa kananan yara na MDD wato UNICEF yana tallafa mana a kowane wata da kudin ciyarwa, amma a gaskiya yawancin kudadenmu na tafiya ne a fannin kiwon lafiya, don haka ziyarar da likitocin kasar Sin suka kawo mana, ta samar mana da isassun magunguna da a baya, sai mun saya a wuraren sayar da magunguna masu zaman kansu a kan farashi mai tsada.

Boro ta ce, a yayin ziyarar da likitocin kasar Sin suke kaiwa gidajen marayu a wata-wata, suna duba lafiyar yaran baki daya, ta kara da cewa, a wasu lokutan kuma, su kan taimakawa wajen gano matsaloli masu sarkakiya da ba kasafai ake iya gano su ba. (Ibrahim)