logo

HAUSA

Tawagar Kwamitin Sulhu na MDD ta ziyarci Sudan ta Kudu domin ingiza aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta kasar

2021-11-20 15:35:48 CMG

Tawagar Kwamitin Sulhu na MDD ta ziyarci Sudan ta Kudu domin ingiza aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta kasar_fororder_1120-S.Sudan-Faeza

Wata tawagar Kwamitin Sulhu na MDD, ta isa kasar Sudan ta Kudu, domin bibiyar yadda ake aiwatar da yarjejeniyar zama lafiyar da ta kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru ana yi tsakanin bangarori daban daban na jam’iyya mai mulkin kasar.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar Sudan ta Kudu ta fitar, ta ce shugaba Salva Kirr, ya gana da tawagar a ranar Alhamis, inda suka tattauna game da aiwatar da sassan yarjejeniyar zaman lafiyar dake da alaka da tsaro.

Sanarwar ta ruwaito tawagar ta Kwamitin Sulhun na cewa, cimma zaman lafiya hakki ne da ya rataya a wuyan kowa, kana sun yi alkawarin samar da dimbin taimako ga gwamnatin kasar wajen cimma zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Yarjejeniyar wadda aka farfado da ita, ta kai ga kafa gwamnatin riko a kasar, a watan Fabrerun 2020.

Sai dai, har yanzu babban koma bayan da ake fama da shi shi ne, bukatar sake hade kan rundunonin tsaron kasar. (Fa’iza Mustapha) 

Faeza