logo

HAUSA

Za a kaddamar da gagarumin aikin rigakafin COVID-19 a Sudan ta kudu

2021-10-18 09:31:59 CRI

Za a kaddamar da gagarumin aikin rigakafin COVID-19 a Sudan ta kudu_fororder_1018-Saminu1-south Sudan

Mukaddashin shugaban shirin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a Sudan ta kudu John Rumunu, ya ce gwamnatin kasarsa ta shirya kaddamar da gagarumin aikin rigakafin COVID-19 da gwajin cutar, a wani mataki na dakile yaduwar ta.

John Rumunu, wanda ya bayyana hakan a jiya Lahadi, ya kuma ja hankalin al’ummar kasar da su rika kiyaye ka’idojin kiwon lafiya masu nasaba da dakile yaduwar COVID-19, kamar sanya masarufin baki da hanci, da ba da tazara, da wanke hannu a kai a kai, tare da kauracewa cunkoson jama'a.

Wasu rahotanni sun ruwaito shugabar shirin yaki da COVID-19 ta hukumar lafiya ta duniya WHO Sacha Bootsman na cewa, kaso 0.3 bisa dari ne kawai daga al’ummar Sudan ta kudu su miliyan 12.2, suka karbi rigakafin wannan cuta.

Sacha Bootsman ta kara da cewa, sun cimma nasarar yiwa mutane 35,755 rigakafin alluran 120,413, cikin mutum miliyan 2.4 da aka tsara yiwa alluran, aka kuma ayyana hakan tun a watan Afirilu.  (Saminu)