logo

HAUSA

Rasha ta ce kungiyar tsaron NATO ta kara ta’azzara al’amurra a Ukraine

2021-12-16 11:22:27 CRI

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana jiya Laraba cewa, taimakon da kungiyar kawancen tsaro ta NATO ke bayarwa kasar Ukraine ta fannin aikin soja, babu abin da yake haifarwa sai kara ruruta wutar tashin hankali a cikin gidan kasar.

Maria Zakharova, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rashan ta ce, mambobin kasashen kungiyar NATO suna ci gaba da samar da makamai ga Ukraine, suna kuma bayar da horo ga dakarun sojojin kasar, kuma suna yin hakan ne ba domin kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Ukraine ba, sai dai domin kara ruruta wutar rikici a kasar.

A jawabinta yayin taron manema labaru na mako-mako, Maria Zakharova ta bayyana fargabar cewa, wannan mataki zai iya kara jefa kasar Ukraine cikin yakin basasa mafi muni.

A cewarta, kasar Amurka ta samar da tallafin dalar Amurka biliyan 2.5 ga sojojin Ukraine tun daga shekarar 2014, wanda ya hada da sama da dalar Amurka miliyan 400 a wannan shekara kadai.(Ahmad)

Ahmad