logo

HAUSA

Xi Jinping ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Ukraine

2021-07-14 14:27:23 CRI

A daren jiya Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na kasar Ukraine Volodymyr Oleksandrovych Zelensky, inda Xi ya jaddada cewa, ya kamata bangarorin biyu su inganta hadin kansu, wajen raya muhimman ababen more rayuwa, da ma shirin raya harkokin zirga-zirga bisa layin dogo a tsakanin Sin da kasashen Turai, a karkashin inuwar shawarar “ziri daya da hanya daya”.

A nasa bangaren kuwa, Shugaba Zelensky cewa ya yi, kasarsa na bin manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma tana son amfani da damar cika shekaru 10 da kulla dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tare, da ma cika shekaru 30 da kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu, wajen inganta hadin kansu, da cudanyarsu a fannoni daban daban.(Kande Gao)