logo

HAUSA

Xi Jinping ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Turkiyya

2021-07-14 10:26:22 CRI

A daren jiya Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, inda Shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, Sin na son hadin gwiwa tare da Turkiyya a fannin allurar rigakafin cutar COVID-19, a kokarin taimaka wa Turkiyya wajen samun nasara a kan cutar. Sa’an nan ya kamata bangarorin biyu su nuna adawa da sanya siyasa cikin batun neman ganon asalin cutar, da ma daina alakanta kwayoyin cuta da wata kasa, a kokarin raya makomar bil Adama ta bai daya a fannin kiwon lafiya.

A nasa bangaren, Shugaba Erdogan ya ce, ingancin allurar rigakafin COVID-19 da kasar Sin ta samar mata amincewa a sassan duniya, kuma kasarsa na son inganta hadin gwiwa tare da Sin a wannan fannin. Ya ce ko a zamanin da ko a yanzu, da ma a nan gaba, Turkiyya za ta ci gaba da mutunta manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da ma gayon bayan kasar Sin wajen kiyaye ’yancin kanta, da ikon mulkinta, da cikakkun yankunanta, da ma kokarinta na yaki da ta’addanci.(Kande Gao)