logo

HAUSA

Putin da Biden sun tattauna kan Ukraine, dangantakar kasashen biyu, da ma batun Iran

2021-12-08 13:56:38 CRI

Putin da Biden sun tattauna kan Ukraine, dangantakar kasashen biyu, da ma batun Iran_fororder_i04-Putin

Jiya ne, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Joe Biden suka gana ta kafar bidiyo, inda suka tattauna kan rikicin kasar Ukraine, da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma batun yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Wata sanarwa da fadar Kremlin ta kasar Rasha ta fitar, ta ce shugabannin sun fi mayar da hankali ne kan rikicin cikin gida dake faruwa a kasar Ukraine, yayin tattaunawarsu ta biyu cikin watanni shida.

Shugaba Putin ya nemi Biden, ya ba da tabbacin cewa, kungiyar tsaro ta NATO, ba za ta fadada tasirinta zuwa yankin gabashi ba, kuma ba za ta tura makamai kusa da Rasha ba.

A kokarin samar da wasu sharudda don gyara alakar da ke tsakanin kasashen biyu, Putin ya yiwa Biden tayin dage dukkan takunkuman da aka kakabawa ofisoshin diflomasiyyar Rasha da na Amurka.

Shugabannin biyu sun bayyana fatan cewa, za su ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran cikin kyakkyawan ruhi. Har ila yau, sun bayyana kudirinsu na yin aiki tare, don yaki da laifukan da ake aikatawa ta yanar gizo.

Putin da Biden sun kuma amince cewa, kasashen biyu za su ci gaba da tattaunawa da tuntubar da juna a lokutan da suka dace. (Ibrahim Yaya)