logo

HAUSA

Sin ta yi maraba da yadda Ukraine ta sanar da soke sa hannu kan jawabin hadin gwiwa na adawa da Sin

2021-06-27 11:25:05 CRI

A ranar 26 ga wata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya amsa tambayar manema labaru da aka yi kan yadda kasar Ukraine ta soke sa hannu kan jawabin hadin gwiwa na adawa da kasar Sin a yayin taron karo na 47 na kwamitin harkokin hakkin dan Adam na MDD.

Kakakin ya yi nuni da cewa, a yayin taron, kasashe fiye da 90 ne suka bayyana goyon baya da amsa kiran kasar Sin ta hanyoyi daban daban, sun bayyana ra’ayin adalci. Tsirarrun kasashen yammacin duniya sun sake ci tura a yunkurinsu na bata sunan kasar Sin bisa batutuwan Xinjiang, Hong Kong da Tibet. Lamarin da ya nuna cewa, zukatun mutane sun fi amincewa. Yunkurin wadannan kasashen yammacin duniya na tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, matsa wa Sin lamba, da hana ci gaban kasar Sin bisa hujjar kiyaye hakkin dan Adam ba zai samu nasara ba a karshe. 

Kakakin ya ci gaba da cewa, kasar Sin ta lura da cewa, kasar Ukraine ta soke sa hannu kan jawabin hadin gwiwar adawa da Sin a yayin taron. Haka kuma ma’aikatar harkokin wajen Ukraine ta ba da wata sanarwar cewa, ba za ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin ba. Kudurin Ukraine ya bayyana ruhunta na neman ‘yancin kai da zaman kanta, da kuma mutunta  abubuwan gaskiya, lamarin da ya dace da kundin tsarin mulkin MDD da manyan ka’idojin daidaita hulda a tsakanin kasa da kasa, kasar Sin ta yi maraba da hakan. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan