logo

HAUSA

Kotun Musamman Ta Uyghur , Hayaniyar Siyasa

2021-12-10 14:15:32 CRI

Sakamakon goyon baya da taimako na masu adawa da kasar Sin na kasar Amurka, da kasashen yammacin duniya, ya sa babban taron wakilan Uyghur ta duniya, wato “World Uyghur Congress”, wanda ke adawa da kasar Sin, da ma fatan kawo baraka ga kasar Sin, ya kafa kotun musamman ta Uyghur, inda aka yi hayar mazambata, domin su kitsa karya, da nuna shaidu na jabu, a yunkurin su na tada kura a Xinjiang, da shafa wa kasar Sin bakin fenti. Wannan kotu ba ta dace da doka ba, kuma ba a kafa ta kan gaskiya ba. Har ila yau a baya ma, an tono makarkashiyar kotun sau da dama. Kuma yadda kotun ta yanke hukunci na karshe, cike yake da hayaniyar siyasa.

Karya, ko sau dubu aka yi ta dai karya ce, kuma fure take ba ta ‘ya’ya. Kasashen duniya ba za su gaskata karyar ba, kana karya ba za ta dakatar da ci gaba, da wadata, da kwanciyar hankali a Xinjiang ba. Tabbas kimar wannan kotun da ta zube. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan