logo

HAUSA

Amurka Ba Ta Da Hurumin Sukar Xinjiang Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam

2021-10-19 21:14:16 CRI

Kwanan baya, a cikin jawabinsa, shugaban Amurka Joe Biden ya shafa wa Xinjiang kashin kaji, wai an tilasta wa mutane yin aiki a Xinjiang, ya kuma bata sunan kasar Sin dangane da manufar tafiyar da harkokin Xinjiang. Amurka ta soki kasar Sin kan batun hakkin dan Adam, a yunkurin zama shugabar duniya a fannin da’a, amma duniya ta fahimci rashin gaskiyarta da kuma yadda ta ke nuna fuska biyu kan batun hakkin dan Adam.

An lura da cewa, har kullum Amurka ta yi karya kan yadda aka tilasta wa mutane yin aiki a Xinjiang, da kuma aikata kisan kiyashi a jihar, duk da ba ta da shaidu. Ta yi ta sokan Xinjiang kan batun hakkin dan Adam, har ma ta matsa wa kawayenta lamba da su hada baki wajen zargin kasar Sin.

Karya fure take, ba ta ‘ya’ya. Kwanan baya, an bankado yawan kudaden da aka biya masu gabatar da shaidar karya wadanda suka bayyana a gaban kotun musamman ta Uygur a shafin sada zumunta, lamarin da ya sake nuna cewa, batun hakkin dan Adam, wata karya ce ta daban da masu adawa da kasar Sin suka kirkiro, a yunkurin hana ci gaban masana’antun Xinjiang, bartana kwanciyar hankali a Xinjiang da dakatar da bunkasar kasar Sin.

Hakika dai, ba a samu harin ta’addanci a Xinjiang cikin shekaru fiye da 4 da suka wuce sakamakon matakan yaki da ta’addanci da gwamnatin Sin take dauka. Samun tsaro da kwanciyar hankali a jihar, ya aza harsashi mai kyau wajen samun saurin ci gaban tattalin arzikinta. Erken Reyimu, wani mai noman auduga ne a garin Gulebage a gundumar Yuli ta Xinjiang, ya yi girbin auduga a bana. Zai samu kudin shiga har fiye da kudin Sin yuan miliyan 1. Yadda ya ji dadin zamansa, wata alama ce da ta nuna yadda ake kare hakkin dan Adam a Xinjiang.

Bata sunan Xinjiang ba zai iya warware matsalolin da Amurka take fuskanta a gida ba, kana ba zai hana samun wadata da kwanciyar hankali a Xinjiang ba, haka kuma ba zai dakatar da ci gaban kasar Sin ba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan