logo

HAUSA

Yankin Xinjiang Na Fatan Kungiyar Taliban Za Ta Shata Layi Tsakaninta Da ETIM

2021-08-30 19:55:33 CRI

Mai magana da yawun gwamnatin yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa na kasar Sin, Elijan Anayat, ya shaida wa taron manema labaran da aka shirya Litinin din nan, kan batutuwan da suka shafi yankin na Xinjiang cewa, ya kamata kungiyar Taliban ta Afghanistan, ta shata sahihin layi a tsakaninta da kungiyar Islama ta gabashin Turkistan wato ETIM da sauran kungiyoyin ta’addanci, ta kuma yake su yadda ya kamata.

Kakakin ya ce, kasar Sin ce babbar makwabciyar Afghanistan, kuma yankin Xinjiang ya yi iyaki da Afghanistan. A baya, mayakan ‘yan ta’adda, kamar ETIM sun taba taruwa a kasar Afghanistan, lamarin da ya haifar da barazana kai tsaye ga harkokin tsaro da zaman lafiyar yankin Xinjiang na kasar Sin. A don haka, ya yi fatan kungiyar Taliban, za ta yi yaki da ETIM da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda yadda ya kamata.

Elijan Anayat ya kuma bayyana kudirin yankin Xinjiang na yaki da ETIM da sauran mayakan ‘yan ta’adda, domin kare rayuka da dukiyoyin dukkan kabilu, da kiyaye zamantakewa da hadin kan kasa. Kuma duk wani yunkuri na kawo rudani da ma ci gaban yankin Xinjiang, ba zai yi nasara ba.(Ibrahim)

Ibrahim