logo

HAUSA

Labarin wannan iyalin da ya kunshi kabilu 7 da ke zaune cikin lumana

2021-11-22 10:52:40 CRI

Labarin wannan iyalin da ya kunshi kabilu 7 da ke zaune cikin lumana_fororder_Ma Lianhua1

Iyalin Ma Lianhua da suka kunshi kabilu daban-daban, na zaune ne a Tacheng, wani birni dake yankin Ili dake jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin. akwai wani bango a gidan da baki daya hotunan iyalin ne suka lullube shi, wadanda ke nuna sauye-sauyen da iyalin da al’umma suka samu tun daga 1980.

An dauki daya daga cikin hotunan mai launi ne a dakin watsa shirye-shirye na gidan talabijin na kasar Sin na CCTV a 2008, kuma yana nuna mambobin iyalin daga kabilun Han da Kazakh da Hui da Uygur da Russian da Daur da Tatar, suna sanye da kayayyakin gargajiya, suna murmushi.

Iyalin wani misali ne na yadda mutane daga kabilu daban-daban kan zauna tare cikin farin ciki da lumana a jihar Xinjiang. Ko wanne dan iyalin Ma Lianhua, ya bada gudunmuwa kuma ya ci gajiyar ci gaban kasar Sin.

Ma, mai shekaru 59, ita ce ta 5 cikin ‘yan uwan 12. An haifi mahaifinta Ma Zhiqiang da mahaifiyarta Bai Xiuzhen a shekarar 1930. A watan Satumban 1949, rundunar ‘yantar da al’ummar Sinawa ta ‘yantar da jihar Xinjiang. Daga nan kuma, mutanen Xinjiang, da sauran na kasar Sin, suka hada hannu wajen kawo sauyi irin na gurguzu da gina al’ummar gurguzu. Ma Zhiqiang, ya yi aiki a matsayin mai tafinta a wata makaranta, domin taimakawa iyalinsa. Ya kware a harshen Sinanci da na Rasha da Kazakh.

A farko-farkon kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, an yi fama da karancin kayayyakin bukatun yau da kullum. Domin taimakawa wannan babban iyali, sai Ma Zhiqiang da Bai Xiuzhen da yaransu, suka fara shuka masara da dankalin turawa da karas da kabeji a filin gidansu. A ko wane lokacin kaka, Ma Lianhua da yayunta mata kan sayar da dafaffiyar masara a kasuwa domin kara samarwa iyalin kudin shiga.

A wancan lokaci da ake wahala, Ma Lianhua da iyalinta sun more rayuwarsu. A matsayin mai sha’awar fasahohi, mahaifinta na son rera waka da raye raye da zanen fenti. Ma Lianhua na alfahari da mahaifinta. “mahaifina sananne ne a birnin Tacheng saboda yadda ya iya rawa,” a cewarta.

Yanzu Ma Lianhua da ‘yan uwanta duk sun yi aure, kuma rayuwarsu ta kyautatu idan aka kwatanta da lokacin da suke kanana. Galibinsu na zaune a sabbin gidaje, sun sayi motoci. Auren da suka yi ya sa an samu kabilu daban-daban cikin iyalin. Mijin Ma Jinhua, babba a cikinsu, dan kabilar Rasha ne. Matar Ma Jinyong, da na 2 a gidan, ‘yar kabilar Han ce. Matar Ma Jinfeng, da na 4 a gidan, ‘yar kabilar Uygur ce. Iyayen Ma Lianhua, wadanda suka tarbiyantar da su zama masu fahimta, su ne suka yi maraba da kabilun daban-daban, kuma musammam saboda kauna da girmamawa da ake wa juna a iyalin da ya kunshi kabilu daban-daban.

“A cewar iyayena, dole ne mu mutunta tare da fahimtar juna. Ta hakan ne kadai za mu zauna cikin lumana da farin ciki,” cewar Ma Lianhua. Ta kara da cewa, iyalin kan yi murnar dukkan muhimman bukukuwan gargajiya a tare.

A irin wannan babban iyali dake da kabilu daban-daban, dukkansu na jituwa da juna, kanana na girmama manya, yayin da manyan ke nuna kauna da tausayi ga kananan.

Labarin wannan iyalin da ya kunshi kabilu 7 da ke zaune cikin lumana_fororder_Ma Lianhua2

Labarin wannan iyalin da ya kunshi kabilu 7 da ke zaune cikin lumana, sananne ne a Tacheng.

A lokacin bazarar shekarar 2008, mahaifin Ma Lianhua ya kamu da rashin lafiya. Da rana Ma Lianhua kan je aiki, da dare, ta ziyarci mahaifinta a asibiti, ta kuma wanke kayayyakinsa. Makwabtansu na yaba mata tare da ‘yan uwanta, saboda yadda suke kula da mahaifinsu.

Bayan rasuwar mahaifinta, lafiyar mahaifiyar Ma Lianhua ya kara tabarbarewa. Sai dai, a kowanne lokaci, da Madam Bai ta ga ‘ya’ya da jikokinta, ta kan yi farin ciki. Tana kaunar yadda iyalin ke zaune cikin lumana tana kuma yabawa da yadda suke kaunarta tare da kulawa da ita.

A shekarar 2010, da taimakon hukumar lafiya ta Xinjiang, da kuma cibiyar lafiya ta Tacheng, aka kwantar da Madam Bai a asibitin koyarwa na Jami’ar nazarin likitanci na Xinjiang, inda aka duba lafiyarta.

Labaran wannan iyali sanannu ne, kuma Ma Lianhua ta samu lambobin yabo da dama saboda kulawar da ta yi da iyaye da ‘yan uwanta.

Teburin talabijin dinta cike yake da takardun shaida da lambobin yabo da dama da ta samu, ciki har da guda 2 da jihar Xinjiang ta ba ta.  

Jihar Xinjiang ta samu ci gaba da dama a shekarun baya-bayan nan, saboda dabarun JKS da gwamnatin jihar. Rayuwar mazauna na ta kyautatuwa, ciki har da na iyalin Ma.

A yau, galibin matasa na iyalin sun kammala karatu a jami’a, kuma suna da tsayayyen aiki kamar malanta ko jami’an ‘yan sanda ko masu rawa.

Yanzu, akwai sama da mutane 60 cikin iyalin Ma, wasu suna Tacheng, yayin da wasu ke Urumqi ko Karamay, wasu kuma sun yi nisa suna birnin Yinchuan na jihar Ningxia ko birnin Qingdao na lardin Shandong da ke gabashin kasar Sin.

Duk da ba sa haduwa da juna akai-akai, suna kasancewa tare ta kafar WeChat kusan kullum. Ci gaban da aka samu a fannin fasaha ya saukaka zumunci.

A cewar Ma, “kasarmu na samun ci gaba a kullum, haka ma iyalina. Muna yawaba JKS da ma kasarmu. Ta hanyar bin Jam’iyya, za mu rayu cikin farin ciki.”

Kande