He Jiaolong: Kokarin yada al’adu da sha’anin yawon shakatawa na jihar Xinjiang a matsayinta na tauraruwar dandalin sada zumunta
2021-08-30 16:31:36 CRI
He Jiaolong, tsohuwar mataimakiyar shugaban gundumar Zhaosu ta yankin Ili na kabilar Kazak mai cin gashin kansa na jihar Xinjiang dake arewa maso yammacin kasar Sin, ta yi fice ne a watan Nuwamban 2020, a lokacin da ta bayyana cikin wani gajeren bidiyo tana sukuwa kan doki a cikin dusar kankara, da nufin yayata wuraren yawon bude ido na yankin. Cikin kasa da shekara bayan ta fara sayar da kayayyakin da suka fi shahara a yankin, kai tsaye ta kafar bidiyo, ta samu mabiya miliyan 2.86 a dandalin wallafa gajeren bidiyo na Douyin, kuma ta taimaka wajen sayar da kayayyakin da darajarsu ta kai sama da yuan miliyan 10, kwatankwacin dala miliyan 1.54. Ta kuma tsara shirye-shiye da dama da suka amfanawa mazauna yankin.
A watan Afrilu na shekarar da muke ciki, aka ayyana He a matsayin mataimakiyar shugaban ofishin raya al’adu da yawon bude ido na yankin Ili. Tun daga watan Nuwamban bara da bidiyonta ya yi fice, He ta yi amfani da wannan dama wajen yayata kayayyakin yankin da kuma wuraren yawon bude ido.
Ta ce, “ya kamata mu yi amfani da dimbin mabiyan dake dandalin sada zumunta. Muna bukatar inganta hidimomin yawon bude ido da sauran abubuwan da suke da alaka da shi, da kuma amfana daga albarkatun halitta. Ta wannan hanya ne kadai za mu iya samun aminci daga masu yawon bude ido da tabbatar da mutane sun jima suna sha’awar yankinmu.”
Sa’an nan He ta kara da cewa, “A baya, ba na son sunan ‘tauraruwar kafar sada zumunta’, amma yanzu na amince da shi. Zama tauraruwa a dandalin sada zumunta ya kara min nauyi sosai. Amma mutanen yankinmu kan fada min cewa, ‘ban san me ake nufi da tauraruwar dandalin sada zumunta ba. Amma a kanki, na san me yake nufi, wato mai taimakawa jama’a sayar da kayayykinsu, ita ce mai yin abubuwan da za su yayata mahaifarta.’ Jin hakan ne ya ba ni kwarin gwiwar amincewa da sunan tauraruwar kafar sada zumunta.”
An gudanar da taron baje kolin kayayyakin gona da sauran wasu kayayyaki a yankin Ili a ranar 20 ga watan Mayun shekarar 2020. Inda aka bukaci ko wanne birni da gunduma a yankin ya gabatar da jami’in da zai tallata tare da sayar da kayayyakinsa a dandalin Douyin ta shirin bidiyo na kai tsaye. A matsayin mataimakiyar shugaban gundumar Zhaosu, kuma sakatariyar mambobin JKS a ofishin kula da harkokin gona da na karkara na gundumar, an zabi He Jiaolong a matsayin wadda za ta tallata tare da sayar da kayayyakin da aka samar a Zhaosu.
A matsayin sabuwa a fagen amfani da dandalin Douyin, He ba ta da mabiya masu yawa da farko. Amma domin ta ja hankalinsu, sai ta fara tsara gajerun bidiyo masu inganci da shirin kai tsaye akai-akai. A kowanne shirin bidiyo na kai tsaye, ta kan samu sabbin mabiya tsakanin 500 zuwa 2,000. Cikin ‘yan watanni, He ta samu kimanin mabiya dubu 200. Me ya kawowa He daukaka haka cikin kankanin lokaci? Gajeren bidiyon da ta yi a kan doki a cikin dusar kankara ne. He ta gaya mana cewa, “a lokacin, wasu taurarin dandalin sada zumunta biyu sun ziyarci Xinjiang. Dukkansu kuma suna da kimanin mabiya miliyan 1 kuma gajerun bidiyonsu sun yi fice a Douyin. Ana yi wa Zhaosu lakabi da “garin dawaki”, don haka na gayyace su Zhaosu tare da daukar gajerun bidiyo domin taimaka mana tallata wuraren bude ido. ”
A ranar da suka dauki gajerun bidiyon, sun hau dawaki tare. Sukuwa wata fasaha ce da dukkan jami’an kauyuka a Xinjinag ke da shi, ciki kuwa har da He Jiaolong. Ta kware sosai. Sanye da farar malafa da jar riga, ta yi kama da wata jarumar gargajiya.
Nan da nan bayan wallafa gajerun bidiyon, ya ja hankalin masu amfani da shafin intanet, da yawa daga cikinsu sun rubuta “tana da kwarjini” ko kuma “Zhaosu wuri ne mai kyau, Ina son zuwa”. Ba jimawa, adadin mabiyanta ya zarce miliyan 1 zuwa miliyan 2.
Yawan mabiyan He Jiaolong ya kawo sauyi ga gundumar Zhaosu. Bidiyon da take yi kai tsaye da wadanda take wallafawa sun taimaka mata bunkasa bangaren yawon shakatawa na yankin. An samu karuwar masu yawon bude ido dake ziyartar gundumar cikin watannin da suka gabata.
Kayayyakin da He take sayarwa duka yayin bidiyonta na kai tsaye, sun hada da zuma da chukwi da man canola da taliyar shinkafa, wadanda ake kira da abubuwa masu daraja 4 na Zhaosu. Cinikin da take yi a bidiyo na kai tsaye guda 1 kan zarce yuan miliyan 2, kwatankwacin dala dubu 300. Zuwa yanzu, saboda ficen da He ta yi, an sayar da kayayyakin gona da sauran kayayyaki da darajarsu ta kai sama da miliyan 10 kwatankwacin dala miliyan 1.54.
Ganin murmushin mutanen yankin ne abu mafi gamsuwa a wajen He Jiaolong. “Manya kan yaba min, suna cewa ‘muna goyon bayanki’ a lokacin da suka hadu da ni. Wasu lokuta, idan ina cin abinci a dakin sayar da abinci, masu wurin kan ce, ‘ki zo ki ci abinci kyauta a duk lokacin da kike so.’ dole ne in biya kudi, amma kalamansu kan faranta mini rai. Farin cikin mutanen ne ke ba ni kwarin gwiwa,” cewar He.
Ta kan yi amfani da kusan dukkan lokacin da ba ta da aiki wajen yin shirin bidiyo na kai tsaye da daukar gajerun bidiyo. Wani lokaci, domin samar da gajerun bidiyo masu inganci, ta kan bar gida da asuba domin daukar bidiyo a wurare masu nisa, wani lokaci sai ta kai tsakar dare tana aikin gyaran bidiyo. Zuwa ranar 23 ga watan Afrilu, He ta fitar da gajerun bidiyo 216 a kan Douyin, kuma wadannan bidiyo sun ja hankalin mabiya miliyan 2.93 tare da samun wadanda suka danna “like” sama da miliyan 9.85.
A lokacin da aka kaddamar da dandalin yada labarai na We-media matrix da na cinikayya ta intanet a gundumar Zhaosu, He Jiaolong ta samu goyon baya sosai daga masu amfani da intanet dake fadin kasar.
Wasu masu amfani da intanet sun taimaka wajen kula da wasu ayyukan shafin domin tattaunawa da tuntubar kwastomomi da masu sayar da kayayyaki da kamfanonin jigilar kayayyaki. Sun fada mata cewa, tana ba al’umma kwarin gwiwa kuma tana nuna nagartar ma’aikatan gwamnati, shi ya sa suke son taimaka mata.
A matsayin mambar JKS, He Jiaolong ta kan sanya tambarin jam’iyyar a duk lokacin da take shirin bidiyo na kai tsaye. Ta ce tana alfahari da kasancewarta ‘yar jam’iyyar. “Ina farin cikin samun damar bayyana kwarewata a dandalin sada zumunta, da kuma taimakawa mutane masu bukata”, cewarta.
Haka kuma, He Jiaolong ta ce za ta ci gaba da inganta kwarewarta. “Ina shirin kafa wani dandalin we-media matrix da taurarin kafar sada zumunta don mu hada hannu wajen tallata kyawawan wuraren bude ido da albarkatun dake akwai a yankin Ili na kabilar Kazak mai cin ganshin kansa.”(Kande Gao)