logo

HAUSA

Demokuradiyyar Kasar Sin

2021-12-04 19:49:53 CRI

Demokuradiyyar Kasar Sin_fororder_sin

Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da wata takardar bayani mai suna “Demokuradiyyar Kasar Sin” a yau Asabar, inda aka yi cikakken bayani kan tunanin kasar Sin dangane da demokuradiyya, fasalin da tsari, da nasarorinta, tare da nuni da cewa, demokuradiyyar kasar Sin, demokuradiyya ce ta al’umma, wato al’umma ne jigo da ginshikin harkokin kasar.

Akwai hanyoyi daban daban da ake bi domin samun demokuradiyya. Hanya mafi kyau da wata kasa zata bi, ita ce hanya mafi dacewa da ita. Ko wata kasa tana bin hanyar demokuradiyya ko a’a, ya danganta da ko al’umma ne jigo da ginshikin harkokin kasar ko a’a.

Alal misali, ana zabar wakilan jama’a a matakai daban daban a nan kasar Sin ta hanyoyi guda 2, wato kai tsaye da kuma ba na kai tsaye ba. A cikin dukkan wakilan jama’ar, wasu daga mabambantan gundumumi na samun rinjaye, wato al’umma ne suka zabe su kai tsaye. Ban da haka kuma, an tsai da dukkan kudurorin da suka shafi kafa doka a kasar Sin bisa ajandar da aka tsara, kuma ta hanyar demokuradiyya da kimiyya, bayan da aka tattauna tsakanin al’umma. Ma iya cewa, dangane da manufofin kasar, da tafiyar da harkokin zamantakewar al’ummar kasa, da kuma zaman yau da kullum, jama’ar Sin suna fadin albarkacin bakinsu ne kan bukatunsu, kana ana sauraron bukatunsu, sa’an nan ana mayar da martani kan bukatunsu. Kamar yadda Charles Onunaiju, darektan cibiyar nazarin kasar Sin ta kasar Najeriya ya fada, lalle kasar Sin ta samu wata hanyar demokuradiyya mai dacewa da halinta da kuma jama’arta.

Demokuradiyya ta sha bamban a kasa da kasa, kana kasa da kasa ta sha bamban da juna. Demokuradiyyar kasar Sin ya shaida cewa, demokuradiyyar kasashen yammacin duniya, ba ita ce kadai demokuradiyya a duniya ba, kuma ba ta dace da kowa ba. Kasashen yammacin duniya ba su da iznin bayyana ma’anar demokuradiyya, ba su kuma da iznin tantance demokuradiyya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan