logo

HAUSA

Sin: Demokuradiyyar Amurka kogi ce maras tushe

2021-12-03 19:39:20 CRI

Sin: Demokuradiyyar Amurka kogi ce maras tushe_fororder_赵立坚

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya shaidawa taron manema labarai da aka saba shiryawa Juma'ar nan cewa, demokuradiyyar Amurka ta dade da zama ta kogi maras tushe, kuma jama’a ma ta dade da juya mata baya.

Zhao ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga wani bincike da jami'ar Harvard ta gudanar, wanda ya nuna rashin amincewa da demokuradiyyar Amurka a tsakanin matasan kasar

Alkaluman bincike sun nuna cewa, kashi 7 cikin 100 ne kawai ke kallon Amurka a matsayin mai tafiyar da tsafatacciyar demokradiyya, yayin da kashi 52 cikin 100 suka yi imanin cewa, demokuradiyyar kasar na “cikin matsala” ko kuma ta “gaza”.

A dangane da wannan rahoto, Zhao ya ce demokuradiyyar Amurka wata dabara ce ta yaudarar 'yan kasarta dake cikin gida, kuma wani makami ne ta aiwatar da mulkinta na danniya a kasashen waje.(Ibrahim)

Ibrahim