logo

HAUSA

Amurka Ba Ta Da Iznin Bayyana Ma’anar Demokuradiyya

2021-11-29 22:03:21 CRI

Amurka Ba Ta Da Iznin Bayyana Ma’anar Demokuradiyya

Jakadun Sin da Rasha dake kasar Amurka sun rubuta bayanin hadin gwiwa a mujallar The National Interest ta kasar Amurka a kwanakin baya, inda suka nuna adawa da kasar Amurka kan yadda ta kira wai "Taron kolin dimokuradiyya ", wanda ya jawo hankalin kasa da kasa.

Kasashen duniya sun fahimci cewa, "Taron kolin dimokuradiyya " da aka shirya gudanarwa tun daga ranar 9 zuwa 10 ga watan Disamba, wani yunkuri ne na kasar Amurka na tada rikice-rikice, da haifar da baraka, da tabbatar da manufarta ta kama karya, kana hadari ne da zai haifar da ra’ayin yakin cacar baka. Kasar Amurka ta kan yi amfani da demokuradiyya wajen gudanar da ayyukanta da suka sabawa demokuradiyya.

Rahoton da hukumar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin ta gabatar, na nuna cewa, tun lokacin da aka kawo karshen yakin duniya na biyu zuwa shekarar 2001, an samu rikice-rikice 248 a yankuna 153 na duniya, guda 201 daga cikinsu kasar Amurka ce ta tada su, yawansu ya kai kashi 81 cikin dari na adadinsa. Kasar Amurka ta aiwatar da wata manufa wai kyautata yanayin demokuradiyya, wadda ta haddasa mutuwa da raunatar fararen hula da haddasa hasarori, lamarin da cusa kasashen da abin ya shafa shiga yanayin fuskantar rikice-rikice na dogon lokaci.

Demokuradiyya daraja ce da kasa da kasa suke neman samun ta, ba hanyar cimma yunkurin siyasa na kasar Amurka ba ce. A sakamakon kaiwa wasu kasashe hare-hare, da haifar da baraka ga wasu yankuna, gwamnatin kasar Amurka ba ta da iznin bayyana ma’anar demokuradiyya. "Taron kolin dimokuradiyya" da za a gudanar tamkar wani wasan kwaikwayo mai ban dariya. Babu shakka kasar Amurka ba za ta cimma yunkurinta na kama karya ta hanyar amfani da dalilai na demokuradiyya ba. (Zainab)