logo

HAUSA

Wajibi Ne Amurka Ta Warware Matsalar Kisan Kare Dangi A Gida Kafin Ta Shirya Taron Kolin Demokuradiyya

2021-12-02 20:45:32 CRI

Wajibi Ne Amurka Ta Warware Matsalar Kisan Kare Dangi A Gida Kafin Ta Shirya Taron Kolin Demokuradiyya_fororder_amurka

A ranar sallar cika ciki wato Thanksgiving Day, wasu mambobin kabilun ‘yan asalin nahiyar Amurka daga yankin New England a arewa maso gabashin kasar Amurka sun yi gangami, don tunawa da kisan kare dangi da aka yi wa miliyoyin ‘yan asalin nahiyar Amurka tare da kwace gonakinsu da kuma lalata al’adunsu, lamarin da aka yi ba’a sosai kan yadda fararen fata Amurkawa suka kafa ranar sallar cika ciki wato Thanksgiving Day domin nuna godiya ga yadda Indiyawan daji suka cece su a baya.

Bai kamata ‘Yan siyasan Amurka da suke kokarin shirya taron kolin demokuradiyya su yi kunnen uwar shegu da zargin da ‘yan asalin nahiyar Amurka suka yi ba. Idan suna son shirya wannan taron kolin demokuradiyya, to, ya kamata su fara warware matsalar kisan kare dangi a cikin gida.

Sakamakon binciken ra’ayoyin jama’a da cibiyar nazari ta Pew ta gabatar a karshen watan Oktoban bana ya nuna cewa, kaso 74 cikin 100 na Amurkawa na ganin cewa, matsalar wariyar launin fata, wata mummunar matsala ce a Amurka. Haka kuma, shugabannin Amurka su ma sun amince da cewa, matsalar wariyar launin fata bisa tsari, ta zama ruwan dare a kasar. Matsalar wariyar launin fata da ke bazuwa a ko ina a Amurka, wata babbar matsala ce da ke nuna cewa, demokuradiyya irin ta Amurka ba ta samu nasara ba. Sakamakon binciken ra’ayoyin jama’a na daban da cibiyar nazarin siyasa ta kwalejin John F. Kennedy a jami’ar Harvard ta gabatar a kwanan baya ya nuna cewa, kaso 52 cikin 100 na matasa a Amurka suna ganin cewa, demokuradiyyar Amurka ta shiga mawuyacin hali ko kuma ba ta samu nasara ba.

Lalle demokuradiyyar Amurka ta bata wa Amurkawa rai. Shin me ya sa gwamnatin Amurka ta tsara shirya taron kolin demokuradiyya? Duk da cewa, ‘yan siyasan Amurka sun yi karya kan demokuradiyya, amma ba za su boye matsalar wariyar launin fata, kawo baraka a tsakanin al’ummomi da karuwar gibin da ke tsakanin matalauta da masu kudi ba. Tabbas yunkurin Amurka na warware matsalolinta ta hanyar shirya taron kolin demokuradiyya, ba zai samu nasara ba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan