logo

HAUSA

Ko ‘Yan Siyasan Amurka Za Su Gayyaci Jama’ar Afghanistan A Taron Kolin Demokuradiyya?

2021-12-01 21:22:09 CRI

Ko ‘Yan Siyasan Amurka Za Su Gayyaci Jama’ar Afghanistan A Taron Kolin Demokuradiyya?_fororder_amurka

Kamar yadda Zemarai Qurbanzada, wani dan kasar Afghanistan ya fada, “ko da Amurka ta biya ni diyya, dana ba zai dawo ba. Idan har Amurka ta damu da rayukan mutane da hakkin dan Adam, to, ta kama wadanda suka aikata laifi!” A watan Agustan bana, bayan da aka kai hari kan sojojin kasashen waje da kasar Amurka ke jagoranta a filin jirgin saman kasa da kasa na Kabul, inda sojojin suka bude wuta kan fararen hula, har Zemarai Qurbanzada ya rasa dansa har abada.

Ya zuwa yanzu ba a gurfanar da sojojin Amurka da suka kashe wadanda ba su ji ba, ba su gani ba a Afghanistan. Don haka mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Ryabkov ya ayyana taron kolin demokuradiyya da Amurka za ta kira a matsayin rashin kunya. Mutane na mamakin cewa, ko ‘yan siyasan Amurka za su gayyaci iyalan ‘yan Afghanistan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon bude wutan da sojojin Amurka suka yi, don su bayyana ra’ayoyinsu a taron?

Amurka ba ta gayyaci Afghanistan zuwa taron kolin demokuradiyya din ba, wadda ta yi mata kwaskwarima ta hanyar demokuradiyya, amma a karshe dai ta yi watsi da ita. Lalle wannan abun dariya ne. Amurka ba ta samu nasarar shimfida demokuradiyya a Afghanistan ba, amma ta yi shelar kiran taron kolin demokuradiyya, lamarin da ya sa kasashen duniya kara fahimtar cewa, Amurka ta yi katsa landan ta fuskar aikin soja a wasu kasashe da sunan demokuradiyya. Ainihin dalilin da ya sa Amurka ta kira taron kolin demokuradiyya shi ne domin neman kawo baraka a maimakon kara azama kan demokuradiyya.

Idan Amurka ta damu da demokuradiyya da hakkin dan Adam, to, wajibi ne ta gayyaci iyalan ‘yan Afghanistan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon bude wutan da sojojinta suka yi. Ta haka kasashen duniya za su san abun da Amurka ta kawo wa Afghanistan bayan da ta shafe shekaru 20 tana yi wa Afghanistan kwaskwarima ta hanyar demokuradiyya. Kamar yadda wani masanin hakkin dan Adam na Afghanistan ya fada, ya kamata Amurka ta gayyaci jama’ar Afghanistan da su halarci taron kolin demokuradiyya. Sannan bai dace ta yayata demokuradiyyarta ta hanyar amfani da jinin jama’ar Afghanistan da kuma makomar Afghanistan maras haske ba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan