logo

HAUSA

Takunkumin haramta amfani da kayayyakin sola na kasar Sin ya jefe Amurka cikin rudani

2021-11-14 16:31:38 CMG

Takunkumin haramta amfani da kayayyakin sola na kasar Sin ya jefe Amurka cikin rudani_fororder_1114-Amurka-Solar-Ahmad

Wani kamfanin Amurka ya bayyanawa gidan talabijin na Bloomberg na kasar Amurka kwanan nan cewa, kasar Amurka ta shiga yanayi na tsaka mai wuya a kokarin cimma muradunta game da batun sauyin yanayi, yayin da take kokarin haramta shigo da na’urorin samar da lantarki mai amfani da hasken rana wato sola daga kasar Sin.

Haramcin ya haifar da matsaloli na rashin samun mallakar kayayyakin na’urorin a farashi mai sauki, kamar yadda Ronen Faier, babban jami’in sashen kudi na kamfanin fasahar SolarEdge ya bayyana.

Kamfanin SolarEdge, wanda helkwatarsa ke kasar Israel, shi ne yake samar da kayayyakin na’urar wanda ya hada da na’urar inbata, wacce take tura karfin hasken rana daga cikin farantai zuwa tashar bayar da hasken lantarkin.(Ahmad)

Ahmad