logo

HAUSA

"Taron kolin dimokuradiyya" da Amurka ta yi ya kamata ya yi bincike kan al'amuran dimokuradiyya na kasar ita kanta.

2021-11-25 20:25:56 cri

"Taron kolin dimokuradiyya" da Amurka ta yi ya kamata ya yi bincike kan al'amuran dimokuradiyya na kasar ita kanta._fororder_下载 (2)

Shugaban kwamitin tsaro da yaki da cin hanci da rashawa na majalisar Duma ta kasar Rasha, ya bayyana a yayin zama na 7, na kwamitin hadin gwiwar majalisar wakilan jama'ar Sin da Rasha da aka shirya a ranar 23 ga wata cewa, nufin Amurka na shirya taron da take kira wai "Taron kolin dimokuradiyya " shi ne, raba kan al'ummun duniya zuwa nasu da bare, tare da haifar da baraka.

Game da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Alhamis cewa, ainihin burin Amurka na kiran wai "Taron kolin dimokuradiyya" ya kara fitowa fili a gaban kasashen duniya. "Dimokradiyya ba hakkin wata kasa daya kadai ba ne, illa dai kimar bai daya ce ta dukkan bil'adama. Irin tsarin dimokuradiyya, da kuma hanyar da za a bi wajen samun dimokuradiyya ba lallai ya zama iri daya ba ne. Babu wata kasa da ke da hakkin rike ma'ana da yanke hukunci kan dimokaradiyya." (Bilkisu)