logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin zai gudanar da taro na 6 na "1+6" da shugabannin manyan kungiyoyin tattalin arziki na duniya

2021-12-02 19:58:57 CRI

Firaministan kasar Sin zai gudanar da taro na 6 na "1+6" da shugabannin manyan kungiyoyin tattalin arziki na duniya_fororder_lkq

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya sanar a yau Alhamis cewa, firaministan kasar Sin Li Keqiang, zai gudanar da taro na 6 na "1+6" a ranar 6 ga watan Disamba tare da shugabannin manyan kungiyoyin tattalin arziki na kasa da kasa, ta kafar bidiyo daga nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Wang ya shaidawa taron manema labaran da aka saba shiryawa na yau da kullum cewa, shugaban rukunin babban bankin duniya David Malpass, da babbar darektar asusun bayar da lamuni ta duniya Kristalina Georgieva, da Ngozi Okonjo-Iweala, babbar darektar kungiyar cinikayya ta duniya, da Guy Ryder, darekta-janar na kungiyar kwadago ta duniya, da Mathias Cormann, babban sakataren kungiyar hadin kan tattalin arziki da raya kasa, da Klaas Knot, shugaban hukumar kula da harkokin kudi, za su halarci taron

A cewar Wang Wenbin, taken taron shi ne "Samar da bunkasar tattalin arzikin duniya mai karfi da zai kunshi kowa da kuma dorewa: daga farfadowa zuwa sake fasalin kasa", za dai a gudanar da tattaunawa da mu'amala da juna kan batutuwa da dama da suka hada da yanayin tattalin arzikin duniya, da tsarin tafiyar da tattalin arzikin duniya, da kuma kudurin kasar Sin na sa kaimi ga samun bunkasuwa mai inganci ta hanyar yin gyare-gyare, da bude kofa.(Ibrahim)

Ibrahim