logo

HAUSA

Li Keqiang ya bukaci a karfafa hadin gwiwa tsakanin kananan hukumomin Sin da na kasashen Afirka

2021-11-17 10:39:33 CRI

Li Keqiang ya bukaci a karfafa hadin gwiwa tsakanin kananan hukumomin Sin da na kasashen Afirka_fororder_211117-Li Keqiang

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bukaci a karfafa, tare da fadada hadin gwiwa mai ma’ana tsakanin kananan hukumomin Sin da na kasashen Afirka, domin samar da kyakkyawar makoma ga al’ummun Sin biliyan 2.7, da takwarorinsu na kasashen Afirka.

Li ya bayyana hakan ne, cikin jawabinsa a dandali na 4 na hadin gwiwar kananan hukumomin Sin da na kasashen nahiyar Afirka wanda ya gudana ta kafar bidiyo. Firaministan na Sin ya ce ba mai iya dakushe tasirin kawancen dake tsakanin Sin da Afirka, kuma Sin a shirye take ta kara fadada tallafin rigakafi, da sauran kayayyakin yaki da annobar COVID-19 ga kasashen Afirka gwargwadon bukatunsu, matakin dake da nufin gina garkuwa mai karfi ta kare lafiyar al’ummun nahiyar.

Kaza lika firaminista Li ya ce, Sin na fatan daidaita salon ci gabanta da na takwarorin ta dake Afirka, da karfafa musayar kwarewar samar da ci gaba a fannin jagorancin raya birane, da yaki da talauci, da gina zamantakewar al’umma, da zamanintar da ayyukan noma, da ingiza hadin gwiwar kawance tsakanin biranen sassan biyu.

Daga nan sai firaministan na Sin ya bayyana burin kasarsa, na ci gaba da aiki tare da kasashen Afirka, wajen kare moriyar kasashe masu tasowa, da wanzar da kawancen gargajiya mai kunshe da martaba juna, da samar da daidaito, da dunkulewa da hadin gwiwa, da rungumar cudanyar dukkanin sassa, da goyon bayan juna kan batutuwan da suka jibanci jigon muradun su, da abubuwan da suke maida hankali a kan su. (Saminu Hassan)