logo

HAUSA

Li Keqiang ya halarci taron shugabannin ASEAN da kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu karo na 24

2021-10-27 20:07:18 CRI

Li Keqiang ya halarci taron shugabannin ASEAN da kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu karo na 24_fororder_hoto

Yau Laraba, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taron shugabannin kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya, wato ASEAN da na kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu karo na 24, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Cikin jawabin da ya gabatar, Li Keqing ya ce “Za mu inganta farfadowar gabashin Asiya bisa dukkan fannoni, da kiyaye zaman lafiya da wadatar yankin cikin dogon lokaci, domin tabbatar da dauwamammen ci gaban gabashin Asiya cikin yanayin bude kofa ga waje, da kuma yanayin nuna fahimtar juna”. (Maryam)