logo

HAUSA

Li Keqiang: Kasar Sin Za Ta Kafa Cibiyar Sasanta Rikicin Yankin Tare Da AALCO

2021-11-30 19:55:02 CRI

Li Keqiang: Kasar Sin Za Ta Kafa Cibiyar Sasanta Rikicin Yankin Tare Da AALCO_fororder_li

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana a jiya Litinin cewa, kasar Sin za ta kafa wata cibiyar sasantawa ta yanki tare da kungiyar ba da shawara kan harkokin shari'a ta Asiya da Afirka (AALCO) a yankin musamman na Hong Kong, don samar da ingantacciyar hidimar warware takaddama ga kasashen yankin Asiya da Afirka

Li ya bayyana haka ne, a lokacin da ya halarci bikin bude taron shekara-shekara na kungiyar AALCO karo na 59 ta kafar bidiyo.

Ya lura da cewa, kasashen Asiya da Afirka, wadanda yawan al'ummarsu ya kai kashi uku cikin hudu na yawan al'ummar duniya, wani muhimmin karfi ne wajen tabbatar da tsarin dokokin kasa da kasa da aiwatar da tsarin kasancewar bangarori daban-daban. Li ya kuma gabatar da shawarwari guda biyar tare da yin kira ga kungiyar AALCO, da ta kara hada karfin kasashe masu tasowa, da ba da sabbin gudummawa don gina duniya mai inganci.

Wadannan shawarwari biyar da jami’in na kasar Sin ya gabatar su ne: tabbatar da daidaito na hakika da aiwatar da tsarin hadin gwiwa tare, karfafa hadin gwiwa tare don samun moriyar juna; gina wani layin kariya mai karfi daga annobar COVID-19 da kuma karfafa tsarin kula da lafiya na duniya tare; gaggauta kama hanyar samun ci gaba mai dorewa ba tare da gurbata muhalli ba, da tabbatar da gaskiya da adalci da kuma karfafa tsarin dokokin kasa da kasa tare.(Ibrahim)

Ibrahim