logo

HAUSA

Li Keqiang ya halarci taron kolin Asiya da Turai karo na 13

2021-11-25 21:36:18 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya halarci taron koli na Asiya da Turai karo na 13 ta kafar bidiyo, a babban dakin taron jama'a a yau Alhamis, inda ya gabatar da jawabi.

Yayin jawabinsa, Li Keqiang ya bayyana cewa, tsayawa kan ra'ayin bangarori daban-daban, shi ne zabin da ya dace na wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Ya ce a gabar da ake fuskantar kalubale sakamakon yaduwar annobar COVID-19, ya zama dole a karfafa hadin gwiwa a fannin nazarin alluran rigakafi da magunguna.

Li Keqiang ya nuna cewa, tsayawa kan yin mu’amala, da yin koyi da juna, wata muhimmiyar hanya ce ta inganta fahimtar juna tsakanin jama’ar kasashen Asiya da na Turai.

Kana ya jaddada cewa, a yayin da ake fuskantar matsaloli da kalubale, muddin kasashen Asiya da na Turai sun mutunta juna, sun karfafa hadin gwiwa irin na samun nasara tare, da hada kai wajen karfafa samun wadata da ci gaba tare, to ko shakka babu, za a samar da wani sabon halin hadin kai a tsakanin Asiya da Turai. (Bilkisu)