logo

HAUSA

Wang Yi na fatan Sin da Amurka za su share fagen tattaunawar shugabannin kasashen biyu

2021-11-13 16:37:06 CRI

Wang Yi na fatan Sin da Amurka za su share fagen tattaunawar shugabannin kasashen biyu_fororder_sindaAmurka

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya yi kira ga Sin da Amurka, da su share fage domin tabbatar da nasarar tattaunawar da shugabannin kasashen biyu za su yi ta bidiyo, tare da mayar da dangantakar kasashen bisa turba.

Wang Yi, ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken a yau Asabar, jim kadan bayan ya sanar da cewa tattaunawar Shugaba Xi Jinping da takwaransa na Amurka Joe Biden, za ta gudana da safiyar ranar Talata.

Da yake tsokaci game da furucin Amurka kan Taiwan, Wang Yi ya jaddada cewa, tarihi da yanayi na hakika, sun nuna cewa ‘yancin kan Taiwan shi ne barazana mafi girma ga zaman lafiya da tsaron yankin. Ya kuma yi kira ga Amurka da ta tsaya kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, maimakon bada alamun da ba su dace ba, ga masu rajin ‘yantar da Taiwan.

Da yake alkawarin Amurka za ta bayyana ra’ayinta kan dangantakar kasashen biyu ta hanyar mutunta juna, Antony Blinken ya ce yana fatan kasashen biyu, za su aike da sako mai karfi ga duniya ta hanyar tattaunawar. (Fa’iza Mustapha)