logo

HAUSA

Wang Wenbin: Wakilan Sin da na Amurka na tattaunawar kut da kut don gane da shirin ganawar shugabannin kasashen biyu

2021-11-12 20:24:12 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce wakilan Sin da na Amurka, na tattaunawar kut da kut, don gane da shirin ganawar shugabannin kasashen biyu.

Wang ya bayyana hakan ne a Juma’ar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa game da hakan, inda ya ce, “muna fatan bangaren Amurka zai yi aiki tare da na Sin, ta yadda za a kai ga cimma nasarar ganawar jagororin kasashen biyu cikin nasara, tare da kara mayar da alakar sassan biyu kan turba ta gari, ta ci gaba bisa daidaito.” (Saminu)