logo

HAUSA

Masanin Najeriya: Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Wadatar Da Kowa A Kasar Ya Cancanci Kasashe Masu Tasowa Su Koya

2021-11-19 13:07:13 CRI

Masanin Najeriya: Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Wadatar Da Kowa A Kasar Ya Cancanci Kasashe Masu Tasowa Su Koya_fororder_najeriya

“Kasar Sin ta samu nasarar fitar da mutanenta duka daga kangin talauci, tare da ci gaba da farfado da yankunan karkara. Na taba ziyartar wasu kauyukan da ke lardin Zhejiang, wadanda suke kasancewa a matsayin kananan birane yanzu, akwai ababen more rayuwar jama’a masu inganci kamar yadda ake samu a birane. Ana amfani da wuta, ruwa, yanar gizo da ma hanyoyin mota kamar yadda ake fata a wadannan wurare.”

Adekunle Osidipe, wani masanin kasar Najeriya wanda ke aiki a kwalejin nazarin Afirka a jami’ar horas da malamai ta Zhejiang ya bayyana haka yayin da yake zantawa da wakilinmu a kwanan baya.

Sakamakon zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a shekarun baya, Adekunle Osidipe ya kara fahimtar bunkasuwar kasarsa da ma sauye-sauyen da ta samu. A ganinsa, yadda kasar Sin ta shiga ayyukan raya ababen more rayuwar jama’a a Najeriya, yana taimakawa Najeriyar cimma manufar raya kasa, ya kuma ba da babbar gudummawa wajen bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar. Yanzu Najeriya ta kyautata aikin sufuri da zirga-zirga kwarai da gaske.

Adekunle Osidipe ya jinjinawa kyawawan fasahohin da kasar Sin ta gabatar ga kasashen Afirka. Alal misali, ya nuna cewa, a karshen shekarar 2020, kos din Luban wanda kwalejin koyar da fasaha da sana’ar jirgin kasa na Tianjin da jami’ar Abuja suka gudanar cikin hadin gwiwa, ya horas da kwararru masu fasahar wutar lantarki, injuna, gine-gine da dai sauransu, lamarin da ya kara kuzari kan ilmin koyar da fasaha da sana’a da tsarin aikin horaswa na Najeriya, da samar da karin kwararru don raya manyan masana’antun kasar.  (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan