logo

HAUSA

Najeriya ta doke Liberia inda take dab da yin nasara a share fagen shigar gasar cin kofin duniya

2021-11-14 16:28:01 CMG

Najeriya ta doke Liberia inda take dab da yin nasara a share fagen shigar gasar cin kofin duniya_fororder_1114-Nigeria-football-Ahmad(1)

Kungiyar kwallon kafan Najeriya ta tashi da ci 2 da 1 a wasanta da Liberia a ranar Asabar a birnin Tangier, na kasar Morocco, a rukunin C na wasannin share fagen shiga gasar cin kofin duniya na Afrika wanda za a gudanar a kasar Qatar a shekarar 2022.

Kungiyar wasan karkashin jagorancin mai horas da ‘yan wasa Gernot Rohr, tayi nasara kan takwararta ta yammacin Afrika ne a wani bugun daga kai sai mai tsaron gida wanda dan wasanta Victor Osimhen, ya zara kwallon mintoci 15 da fara wasan, yayin da kyaftan kungiyar kwallon kafar Ahmed Musa, ya zura kwallo ta biyu mintoci 94 da fara wasan.

Kungiyar wasan wacce ta lashe kofin kwallon kafan Afrika sau uku tana kan gaba a rukunin C da maki 12.

A wasa na biyu da aka buga a ranar Asabar Praia, kasar Cape Verde tayi nasarar doke jamhuriyar tsakiyar Afrika da ci 2 da 1 inda ta zo ta biyu da maki 10 tana matsayi na biyu bayan Najeriya.

Najeriya da Cape Verde zasu taka leda a ranar Talata a birnin Legas inda za a kammala wasan rukunin C na share fagen neman shiga gasar kofin duniya ta Qatar 2022.

Cape Verde tana matakin tsananin bukatar yin nasara a halin yanzu, yayin da Najeriyar kawai tana bukatar yin canjaras ne domin kaiwa mataki na gaba.(Ahmad)

Ahmad