logo

HAUSA

Ana fargabar gini ya danne mutane 21 a Lagos

2021-11-02 09:26:29 CMG

Ana fargabar gini ya danne mutane 21 a Lagos_fororder_1102-saminu-1

Shugaban sashen tsare tsare na hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya reshen jihar Lagos dake kudancin kasar Ibrahim Farinloye, ya ce ana fargabar wani gini da ya rushe ya binne mutane 21.

Ibrahim Farinloye, wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce an yi nasarar ceto mutum 2 da ran su, daga ginin wanda ake kan aikin sa a kan titin Gerard dake unguwar Ikoyi a jihar ta Lagos. Jami’in ya kara da cewa, akwai yiwuwar wasu karin mutanen na karkashin baraguzan ginin.

Ba a kai ga bayyana dalilin rushewar ginin ba, amma jami’an aikin jin kai na ci gaba da aikin ceto, domin zakulo wadanda mai yiwuwa ginin ya binne.  (Saminu)

Saminu