logo

HAUSA

Najeriya: An dakatar da zirga zirgar jiragen kasa a layin dogo na birnin Abuja zuwa Kaduna sakamakon wata fashewa

2021-10-22 13:04:39 cri

Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya NRC, ta sanar da dakatar da zirga zirgar jiragen kasa, kan layin dogo na birnin Abuja zuwa jihar Kaduna, sakamakon wani hari da ya lalata wani sashe na layin dogon.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban hukumar NRC Fidet Okhiria, ya ce daya daga jiragen kasa dake tafe kan layin dogon ya taka wani abun fashewa a jiya Laraba, wanda hakan ya haifar da lalacewar wani bangare na layin dogon.

Okhiria ya kara da cewa, ya zuwa yanzu, ba a tabbatar da ko Bam ne jirgin kasan ya taka ba ko a’a, sai dai tabbas ya taka wani abun fashewa, amma ba a samu jikkatar ko mutum guda a cikin jirgin kasan ba.  (Saminu)