logo

HAUSA

Najeriya: NDLEA ta cimma manyan nasarori a yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi

2021-10-22 15:02:29 cri

Najeriya: NDLEA ta cimma manyan nasarori a yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi_fororder_src=http___5b0988e595225.cdn.sohucs.com_images_20191126_f759d10aebe54fd08b8f5539a4b223f2.JPG&refer=http___5b0988e595225.cdn.sohucs

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta tarayyar Najeriya ko NDLEA a takaice Muhammed Buba Marwa, ya ce hukumar sa ta cimma manyan nasarori, a yakin da take yi da ta’ammuli da kwayoyi a kasar.

Marwa ya bayyana hakan ne, yayin da yake karin haske game da nasarar da hukumar ta NDLEA ta samu, lokacin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Alhamis.

Jami’in ya ce, a shekarar bana, hukumar ta cafke tarin miyagun kwayoyi a sassan kasar daban daban, ta kuma maida hankali ga dakile yunkurin masu fataucin kwayoyi, da nufin kawo karshen illar da miyagun kwayoyin ke kawowa a kasar.

Marwa ya ce daga ranar 25 ga watan Janairun bana zuwa yanzu, MDLEA ta kashe sama da kilogiram miliyan 2.7 na nau’oin miyagun kwayoyi, ta kuma gabatar da kararraki sama da 5,000 masu alaka da miyagun kwayoyi gaban kuliya.

Kaza lika hukumar ta damke masu fataucin kwayoyi 9,355, ciki har da gaggan masu wannan mummunar sana’a. A hannu guda kuma, an yiwa masu shan miyagun kwayoyi 5,579 jinyar yanayin da suka fada. (Saminu)