logo

HAUSA

Lambobin Yabo Na Gasar Wasannin Olympics Ta Lokacin Hunturu Ta Beijing Da Ta Nakasassu Sun Nuna Al’adun Kasar Sin

2021-10-27 10:52:17 CRI

Lambobin Yabo Na Gasar Wasannin Olympics Ta Lokacin Hunturu Ta Beijing Da Ta Nakasassu Sun Nuna Al’adun Kasar Sin_fororder_wasanni

Jiya Talata da dare ne, aka gabatar da samfurin lambobin yabo na gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing da ta nakasassu ta shekarar 2022, a lokacin da ya rage kwanaki 100 kafin a kaddamar da gasar.

Ana kiran lambobin yabon "Tongxin," wadda ke nufin "tare a matsayin daya," kuma suna dauke da alamomin zobba guda biyar da aka zana falsafar gargajiyar kasar Sin na zaman lafiya tsakanin sararin sama da doron duniyarmu da ’yan Adam. Har ila yau, zobban suna nuna alamar zobban Olympics da kuma ruhin Olympics da ke hada duniya ta hanyar wasanni. An kuma hada wadannan lambobin yabo tare da lambobin yabo na gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008, domin bayyana yadda birnin na Beijing ya samu bakuncin shirya gasar wasannin Olympics har sau biyu.

Hang Hai, jami’in kungiyar masu tsara lambobin yabon, kana shehun malami a kwalejin ilmin fasaha na tsakiya na kasar Sin ya taba shiga aikin tsara lambobin yabo na gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008, ya bayyana cewa, “Zobban suna nuna alamar zobban Olympics, da kuma ruhin Olympics da ke hada duniya ta hanyar wasanni. A kan lambobin yabon, an sassaka tsarin gajimare da dusar kankara, a bayan lambobin yabon kuma, akwai ɗigo 24 dake wakiltar gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi karo na 24. Hoton gaba ɗaya, wanda ya yi kama da taswirar sararin samaniya, yana dauke da fatan ’yan wasa su yi fice kuma su haskaka kamar taurari a wasannin. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan